Shekara guda bayan kawar da mulkin Mursi a Masar | Siyasa | DW | 03.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shekara guda bayan kawar da mulkin Mursi a Masar

Shekara guda da kawo ƙarshen mulkin zaɓaɓɓen shugaban Masar Mohammed Mursi, akwai alamun cewar jam'iyyarsa ta yan uwa musulmi tana farfaɗowa.

default

Shugaban Masar,Abdelfatah Al-Sisi

Dandalin Tahrir a birnin Alƙahira ya ɗauki ɗimi a yammacin ranar 3 ga watan Yuli na shekara ta 2013. Dubban ɗaruruwan 'yan Masar suka ɓarke da sowa da farin ciki, suna rera taken ƙasar ta Masar, saboda bayan tattaunawa mai tsanani da shugabannin siyasa da na jama'a, babban hafsan hafsoshin ƙasar, Janar Abdulfatah Al-Sisi ya kawar da mulkin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Mohammed Mursi ta hanyar aiwatar da juyin mulki. Kafin hakan sai da aka ɗauki watanni masu yawa ana ƙoƙarin samun sulhu tsakanin ƙungiyoyi da ɓangarori masu gaba da juna ta fuskar siyasa a wannan ƙasa.

Ƙaruwar zanga-zanga sakamakon ci gaba da tsare tsohon shugaban ƙasar

Ägypten: Ein Jahr nach Sturz des islamistischen Präsidenten Mohammed Mursi

'Yan zanga-zanga a dandalin Tahrir

A yankin arewacin Masar, wato a Sinai, magoya bayan jam'iyyar 'Yan Uwa Musumi sun ƙara tsananta aiyukan su na hare-hare kan sojoji da 'yan sanda, kuma sune ma ake zarginsu da laifin kai hare-haren na bama-bamai a duk faɗin ƙasar ta Masar. A ɗaya hannun, gwamnati ta ƙiƙkiro wata sabuwar doka wadda a ƙarƙashinta, aka haramta duk wata zanga-zanga a ƙasar, matakin da har ma ya shafi aiyukan ƙungiyoyi masu fafutukar neman sauyi waɗanda sune a shekara ta 2011 suka kafa tushen zanga-zangar da ta kawo ƙarshen mulkin daɗaɗɗen shugaban ƙasa Hosni Mubarak.

Daga ƙasa kuma za a iya sauraron rahoton wandda wakilinmu na Alƙhira Mahmud Azare Yaya ya aiko mana dangane da bikin na cikar shekara guda da faduwar gwamnatin Mursi

Mawallafi: Mahamud Azare Yaya
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin