1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawarwarin Ban Ki-Moon ga warware rikicin Masar

July 11, 2013

Duk da zanga-zangar magoya bayan Mursi, sabbin mahukuntan ƙasar na riƙe da shi kuma sun sake yin sammacin jagororin jam'iyyarsa ta 'yan uwa Musulmi

https://p.dw.com/p/196WO
Bildnummer: 59927292 Datum: 01.07.2013 Copyright: imago/Xinhua United Nations Secretary-General Ban Ki-moon addresses a press conference after attending the opening ceremony of the High-level Segment of United Nations Economic and Social Council (ECOSOC) Substantive Session 2013 in Geneva, Switzerland, July 1, 2013. Ban Ki-moon on Monday called to end the violence in Syria and said that an international conference on Syria was the best chance for reaching a political solution to end the conflicts. (Xinhua/Wang Siwei) (zw) SWITZERLAND-GENEVA-UN-SYRIA PUBLICATIONxNOTxINxCHN people xas x0x 2013 quer premiumd 59927292 Date 01 07 2013 Copyright Imago XINHUA United Nations Secretary General Ban KI Moon addresses a Press Conference After attending The Opening Ceremony of The High Level Segment of United Nations Economic and Social Council ECOSOC Substantive Session 2013 in Geneva Switzerland July 1 2013 Ban KI Moon ON Monday called to End The Violence in Syria and Said Thatcher to International Conference ON Syria what The Best Chance for Reaching a Political Solution to End The conflicts XINHUA Wang Siwei ZW Switzerland Geneva UN Syria PUBLICATIONxNOTxINxCHN Celebrities x0x 2013 horizontal premiumd
Ban Ki MoonHoto: imago/Xinhua

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ya nuna damuwarsa dangane da yadda ake ci gaba da tsare mutane a Masar da kuma sammacin da aka yi wa jagororin ƙungiyar 'yan uwa Musulmi bayan da sojoji suka hamɓarar da mulkin Muhammad Mursi.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito cewa, a wata ganawa da suka yi ta wayar tarho, Mr Ban Ki - Moon ya bayyana wa minisatn harkokin wajen Masar Mohammed Kamal Amr cewa, Majalisar Ɗinkin Duniya ba za ta lamunci wani yunƙuri na yin bita da ƙullin siyasa ko kuma ma mayar da wata Jam'iyya ko al'umma saniyar ware ba a Masar.

Haka nan kuma Mr. Ban ya sake nanata goyon bayansa ga kyawawan fatan da jama'ar Masar ke da shi, kuma a dalilin haka ya yi kira ga duk ɓangarorin da abun ya shafa da su gudanar da tattaunawa na sulhu domin samun mafita mai a'ala.

Mr Ban ya yi wa ministan harkokin wajen Masar ɗin tuni dangane da alhakin da ya rataya a kan ƙasar a matakin ƙasa da ƙasa da kuma buƙatar mutunta 'yancin walwala wanjen ma'amala, da faɗin albarkacin baki da kuma mutunta dokokin ƙasa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh