Shawarar ci gaba da wa'adin mulki | Labarai | DW | 29.09.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shawarar ci gaba da wa'adin mulki

Kwanaki gabanin kammala taron koli da ke shirin shata alkiblar siyasar Chadi, wani kwamiti ya bukaci a kara wa'adin shekaru biyu ga gwamnatin mulkin soji ta wucin gadin kafin a gudanar da zabe

Chadi | Babban taro na kasa a N'Djamena | Mahamat Idriss Deby

Chadi | Babban taro na kasa a N'Djamena | Mahamat Idriss Deby

Kwamitin ya nuna sha'awarsa na ganin an kawar da duk wani shigen da ka iya hana shugaban majalisar koli ta rikon kwarya Janar Mahamat Idriss Déby Itno tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da ke tafe, da kuma ba wa daukacin 'yan Chadi ciki har da sojojin da ke kan karagamar mulki da su tsaya takara a manyan zabukan na gaba ba tare da wata wariya ba.

A tsakiyar watan jiya ne dai bangarorin siyasar Chadi suka soma gudanar da babban taron kolin kasar, watanni 16 bayan da rundunar soji ta sanar da mutuwar Shugaba Idriss Déby a fagen daga.

Duk da rusa kundin tsarin mulki da majaliasar dokoki, magajin Shugaba Deby da ke jan ragamar mulki Mahamat Idriss Déby Itno ya sha alwashin sake mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya ta hanyar shirya zabe.