Sharon ya fara numfashi da kansa a karon farko tun bayan sumar dashi | Labarai | DW | 09.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sharon ya fara numfashi da kansa a karon farko tun bayan sumar dashi

Likitocin dake duba faraministan Israela, Ariel Sharon sun fara dawo da shugaban cikin hayyacin sa bayan da suka sumar dashi, don gudanar da tiyata a kwakwalwar sa.

Babban daraktan asibitin na Hadassah dake birnin kudus, wato Mor Yosef ya tabbatar da cewa ,a karon farko, shugaban kasar ta Israela ya fara numfashi da kansa, wanda hakan ke nuni da cewa kwakwalwar sa ta fara aiki.

Duk da wannan ci gaba da aka samu a cewar babban likitan , Mr Sharon naci gaba da samun taimakon na´urori ne, wajen yin numfashin.

Kwararrun dai a wannan fannin sun tabbatar da cewa kafin a gano irin matsalar data shafi kwakwalwar shugaban na Israela, za a iya daukar kwanaki a nan gaba.

Bugu da kari kwararrun sun kuma yi nuni da cewa abu ne mai wuya Mr Sharon ya koma bakin aikin sa, bisa irin halin da yake faruwa game da lafiyar sa a halin yanzu.

Idan dai za a iya tunawa, Mr Sharon ya samu bugun zuciya ne mai karfi, wanda ya haifar masa da tsinkewar jini a kwakwalwar sa a makon daya gabata, wanda hakan yayi sanadiyyar yi masa tiyata har sau uku a kwakwalwar tasa.