Shari′ar tsaffin jami′an Libiya | Labarai | DW | 15.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shari'ar tsaffin jami'an Libiya

An fara shari'ar tsaffin jami'an gwamnatin Libiya

A kasar Libiya, an fara shar'ar fiye da mutane 30 mambobin tsohuwar gwamnati Marigayi Mu'ammar Gaddafi, amma tuni aka jingine shari'ar zuwa wani lokaci, saboda rashin halartar wasu da ake zargi da suka hada da Seif al-Islam dan tsohon shugaban.

Ranar 27 ga watan Afrilu za a ci gaba da shari'ar, mintoci 40 kawai aka shafe yayin shari'ar ta jiya Litinin (15/04/2014). Ana zargin mutanen da laifukan da aka aiwatar lokacin juyin-juya hali na shekara ta 2011, da ya kawo karshen gwamnatin ta Marigayi Gaddafi ta fiye da shekaru 40. Duk 'ya'yan Marigayi Gaddafi, Saadi Gaddafi da Saif al-Islam ba sa kotun lokacin da aka fara shari'ar, amma Abdullah al-Senussi tsohon jami'in hukumar leken asiri ya gurfana.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu