Shari′ar masu adawa da Mubarak a Masar | Labarai | DW | 22.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shari'ar masu adawa da Mubarak a Masar

Kotun Masar ta yanke hukuncin dauri a gidan maza a kan wasu da suka shiga zanga zangar da ta yi sanadin hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak a shekara ta 2011.

Hakazalika ta caji Ahmed Maher da Ahmed Douma da kuma Mohamed Abdel tarar Euro 5300 kowannesu, kimamin Naira miliyan daya da dubu 60 ke nan. Sai dai tuni kungiyoyi masu zaman kansu suka fara yin tir da wannan hukunci, suna masu dangantashi da wani bita da kulli daga bangaren sojojin da ke rike da madafun iko wadanda kuma suka dasa da tsohon shugaba Mubarak.

Da ma tun a jiya asabar wata kotun ta kara cajin hambararen shugaban Mohamed Morsi da wata sabuwar tuhuma baya ga ta murkushe jama'a lokacin bore da kuma leken asiri domin kaddamar da ayyukan tsaro da aka cajeshi da su tun da farko.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman