Shari′ar manyan hafsoshin soji a Sudan | Labarai | DW | 17.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shari'ar manyan hafsoshin soji a Sudan

Wasu manyan jami'an soji a ƙasar Sudan sun gurfana a gaban kotu bayan da aka cafke su a bara ana zarginsu da yunƙurin hanɓarar da gwamnatin Omar al-Bashir

An ƙaddamar da wata shari'a ta soji a ƙasar Sudan, inda aka gurfanar da wasu dakarun sojin da ake zargin da yunƙurin hamɓarar da gwamnatin ƙasar a bara.

A watan Nuwamban shekarar 2012 ne gwamnatin ta sanar cewa ta cafke wasu mutane 13 a ciki har da wasu manyan jami'an tsaro da tsohon jami'in leƙen asiri, inda ake zarginsu da yunƙurin haddasa husumi a ƙasar da kuma kai hari kan wasu manyan jami'an gwamnati.

Daga cikin waɗanda suka gurfana a gaban kotun yau, akwai Birgadiya Mohammed Ibrahim wanda ya taka muhimmiyar rawa a juyin mulkin da aka yi a ƙasar a shekarar 1989 wanda ya ɗora shugaba Omal al-Bashir mai ci, kan kujerar mulkin ƙasar.

Masharhanta sun ce afkuwan wannan na nuna alamun cewa ana samun ruɗani a gwamnatin na al-Bashir a yanzu haka.

Kawo yanzu dai, Sudan ta fuskanci juyin mulki da yunƙurin juyin mulki sau bakwai a tarihinta mai tsawon shekaru 56

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar