1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar magudin zabe a Kenya

March 12, 2013

Dan takarar adawa a zaben shugaban kasar Kenya ya nemi kotu ta tilastawa hukumar zabe gabatar masa da hujjojin tafka magudi.

https://p.dw.com/p/17vlY
Kenya's Prime Minister and presidential candidate Raila Odinga gives an interview to AFP on January 14, 2013, in his office in Nairobi. Kenya is less than two months away from the first presidential elections since deadly post-poll violence five years ago. While two main candidates -- Uhuru Kenyatta and Raila Odinga -- dominate the race, all six candidates have potential influence, especially if voting goes to a second round run off after the March 4 vote. AFP PHOTO/SIMON MAINA (Photo credit should read SIMON MAINA/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images/AFP

Magoya bayan dan takarar adawa a zaben shugaban kasar Kenya Raila Odinga, sun gabatar da kukansu ga wata babbar kotun kasar, inda suke neman ta tilastawa hukumar zaben kasar da kuma kanfanin na'urar sadarawa ta Safaricom da su mika masa takardun bayanai domin karfafa zargin daya ke yi na cewar an sace kuri'u a lokacin zaben da Mr UHuru Kenyatta ya yi nasara.

Ya zuwa yanzu dai Odinga ya ki amincewa da nasarar da Kenyatta ya samu, amma ya bukaci magoya bayansa su kai zuciya nesa a dai dai lokacin da yake neman adalci daga kotunan kasar. Ya ce ya dauki matakin garzayawa kotun ne domin kaucewa maimaita rikicin daya biyo bayan zaben shugaban kasar Kenya a shekara ta 2007, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama.

Dama kuma kotun duniya da ke hukunta manyan laifukan yaki da ke da mazauni a birnin the Hague na kasar Holland, na tuhumar Kenyatta da hannu a rikicin na 2007.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou