1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar laifukan yaƙi a Yugoslaviya

February 23, 2011

Kotun ƙasa da ƙasa da ke hukunta lafukan yaƙin da suka auku a Kosovo ta yanke hukuncin ƙarshe.

https://p.dw.com/p/10OVU
Vlastimir Djordjevic, shugaban 'yan sandan Serbiya a yaƙin KosovoHoto: AP

Kotun ƙasa da ƙasa da ke hukunta lafukan yaƙi akan Yugoslavia ta gama zagaye na biyar kuma na ƙarshe na shari'ar laifukan yaƙi da suka auku a Kosovo. Kotun ta yanke wa tsohon babban hafsan 'yan sandan Serbiya, Vlastimir Djordjevic hukuncin ɗauri na shekaru 27 a gidan yari bisa rawar da ya taka a ƙoƙarin gusar da wasu ƙabilu na Kosovo. Djordjevic mai shekaru 61 da haifuwa an same shi ne da laifin hanzuga kisan da aka yi wa Albaniyawan Kosovo sama da 700 da kuma korar wasu dubban Albaniyawamn daga Kosovo a shekarar 1999. An cafke shi a Montenegro a watan Yulin shekarar 2007 bayan da ya shafe kusan shekaru huɗu yana gudun shari'a. Lugudan wuta da dakarun NATO suka yi ne dai ya kawo ƙarshen wannan rikici a lardin na Serbiya.

Mawallafiya: Halima Balarba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal