Shari′ar gabar kogi tsakanin Kenya da Somaliya | Labarai | DW | 19.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shari'ar gabar kogi tsakanin Kenya da Somaliya

Kenya ta soki Somaliya kan karar da ta shigar a kotun duniya game da takaddamar iyakar gabar kogi a tsakaninsu

Kasar Kenya ta soki lamirin Somaliya dangane da kai kara da ta yi gaban kotun Majalisar Dinkin Duniya game da rikicin da ke tsakaninsu kan iyakar gabar kogi. Shari'ar kuma da za ta tabbatar da makomar yankin gabar kogin na India mai albarkar mai da iskar gas.

Yayin sauraron karar a kotun ta kasa da kasa, Kenya ta bainyana cewa abin kunya ne da takaici ikrarin da Somaliya ta yi cewa, ta yi kokarin sace muhimman rijiyoyin mai da iskar gas yayin shari'ar wadda aka fara a shekarar 2014.

Karar Kenya da Somaliya ta yi a kotun duniyar wadda ke da mazauninta a Hague, wani yunkuri ne na sake shata iyakar gabar kogin da ya ratsa kasashen biyu, lamarin da ke nufin cewa zai shafi rijiyoyin mai guda ashirin da ke tsakiyar teku mallakin kasar Kenya.

Somalia dai ta ce an kasa yin sulhu a tattaunawar samun masalaha ga takaddamar wadda za ta yi tasiri ga sabbin hanyoyin samun kudin shiga ga kowace daga cikin kasashen biyu makwabtan juna na gabashin Afirka.