Shari′ar farko ta zargin juyin mulki a Turkiya | Labarai | DW | 27.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shari'ar farko ta zargin juyin mulki a Turkiya

Wannan shari'a dai da aka fara saurarenta idan har aka kama wadanda ake zargi da laifi 21 daga cikinsu za su iya fiskantar daurin rai-rai.

A karon farko a birnin Istanbul an fara sauraren karar mutanen da ake zargi da hannu a kitsa juyin mulki da ya gaza nasara a kasar Turkiya ranar Talatan nan, tsofaffin 'yan sanda 29 ne dai suka fara gurfana a gaban kuliya kamar yadda kafafan yada labarai a kasar ta Turkiya su ka bayyana.

Wannan shari'a dai da aka fara saurarenta idan har aka kama wadanda ake zargi da laifi 21 daga cikinsu za su iya fiskantar daurin rai-rai saboda laifi na yunkuri na kifar da gwamnati yayin da sauran takwas kuma za su iya fiskantar dauri na tsawon shekaru 15 a gidan kaso saboda zama mambobi na kungiyoyi da ake zargi da zama na 'yan ta'adda.

Mahukuntan na kasar Turkiya dai na zargin Fethullah Gulen fitaccen malamin addinin Islama dan asalin kasar ta Turkiya da ke samun mafaka a Amirka da kungiyarsa, da zama kanwa uwar gami wajen kitsa juyin mulkin.

Fiye da mutane 40,000 ne dai mahukuntan kasar ta Turkiya su ka kama bisa zargi na alaka da kitsa juyin mulkin da bai nasara ba kamar yadda jami'an su ka nunar.