Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.07.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka

Zaman kaso da shugaban kasar Afirka ta Kudu ya fara da annobar corona a kasashen Nambiya da Afirka ta Kudu da rikicin kasar Habasha, sun dauki hankulan jaridun Jamus.

Südafrika | Jacob Zuma

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cikin sharhinta da ta rubuta mai taken: Jacob Zuma ya fada hannun hukuma, tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudun, ya mika kansa ga 'yansanda. Jaridar ta ce a karshe ko Edward Zuma bai iya hana mahaifinsa shiga gidan kaso ba. Sanye da kayan al'ada na 'yan kabilar Zulu, dan tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ya tsaya kai da fata a kofar gidan mahaifinsa da ke gundumar KwaZulu-Natal a gaban manema labarai, inda ya sha alwashin cewa sai bayan ransa za a iya yin awon gaba da mahaifinsa. Mai shekaru 44 a duniya, Edward Zuma ya yi gargadin cewa babu wani  jami'in dan sanda da ke da damar shiga gidan mahaifin nasa. 

Südafrika Nkandla | Jacob Zuma Verhaftung Anhänger

Magoya bayan Jacob Zuma

Batun cafke Zuma da ya ajiye mulki a shekara ta 2018 sakamakon zargin yin sama da fadi da kudin al'umma, ya tayar da kura a kasar. A makon da ya gabata, daruruwan magoya bayan Zuma sun yi dafifi tare da gudanar da zanga-zangar adawa da kama shi. A ranar Larabar da ta gabata, 'yan sanda sun kasance cikin shirin kota kwana. Motoci sama da 100 na 'yan sandan sun kasance cikin shiri, da nufin kama shugaban kasa na farko a tarihin Afirka ta Kudu da zai yi zaman gidan kaso. A karshe, Zuma ya mika kansa cikin dare. Sai dai ya ki shiga motar 'yan sanda, inda ya hau motarsa ta alfarma cikin rakiyar jami'an tsaronsa. Kawo yanzu babu zanga-zanga, kana babu wani jawabi daga masu nuna tawaye dangane da tsare Jacob Zuma. Kotu ce, ta yankewa Zuma zaman gidan kaso na watannin 15, bayan da ya ki mutunta umarninta na gurfana domin bayar da ba'asi dangane da zargin cin hanci da rashawa da ake masa.


BG Die Welt im Griff von Corona

Namibiya da Afirka ta Kudu na fama da annobar corona

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland ta rubuta sharhinta ne mai taken: Rashin shiri da rashin yin rigakafi cikin halin ni 'yasu. Jaridar ta ce a yanzu Namibiya da Afirka ta Kudu ne sansanin annobar COVID-19 a nahiyar Afirka. A yanzu haka annobar corona karo na uku, ta shiga wadannan kasashe da ke kudancin Afirka da karfin gaske. Adadin wadanda suka kamu da cutar na karuwa a manyan biranen Afirka ta Kudu, ya ninka lokacin da aka samu barkewar karo na biyu a kasar cikin watan Disambar bara da na Janairun bana. A wancan lokaci, tilas asibitoci suka rinka sanya marasa lafiya a tantunan wucin gadi na bayar da agajin gaggawa, a yanzu abin ya ta'azzara. 

Präsident Hage Geingob von Namibia

Shugaba Hage Geingob na kasar Namibiya

Haka abin yake a babban birnin kasar Namibiya, ina a yanzu motocin daukar marasa laifiya suka daina daukarsu, kasancewar babu wani fata ko tabbacin asibitoci za su iya karbar su. Adadin wadanda suka kamu da cutar ya ninka har sau uku da rabi, idan aka kwatanta da wadanda suka kamu a farkon watan Yunin da ya gabata. Shugaban kasar Hage Geingob ya nunar da cewa, mutane hudu cikin kowanne 10 da aka yi wa gwaji na dauke da cutar. Haka abin yake a sauran kasashen yankin kudancin Afirkan, inda adadin wadanda ke dauke da coronan ke karuwa. Gwamnatocin kasashen sun yanke shawarar daukar matakan dakile annobar na bai daya, kamar lokacin da ta barke a karo na biyu. Matakan dai sun hadar da saka dokar zaman gida da rufe gidajen sayar da abinci da takaita tafiye-tafiye tsakanin yankuna da gundumomi a kasashensu.

Jaridar Der Tagesspiegel da ta rubuta nata sharhin kan kasar Habasha mai taken: Habasha na barazanr rushewa, tana mai cewa shugaban kasar da ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel Abiy Ahmed ya gaza, a yanzu yankin Tigray na dab da ballewa. Jaridar ta ce tsare-tsaren Firaminista Abiy Ahmed da ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel sun rushe.

Äthiopien Premierminister Abiy Ahmed

Firaiminista Abiy Ahmed na Habasha

Sojojin gwamnati sun sha mamaki, bayan da suka gaza yin nasara a yankin Tigray. Firaministan kasar ta Habasha ya sha alwashin kawo karshen ayyukan 'yan tawayen yankin da ba sa goyon bayan yanayin mulkinsa tun watanni shidan da suka gabata. Abiy dai ya dauki matakin murkushe shugabannin tawayen da ya ke yi wa kallon babbar barazana ga  mulkinsa da karfin soja. A yanzu zai fuskanci karuwar rikice-rikicen kabilanci, baya ga na 'yan tawayen Tigray.  

A kokarin magance matsalar da kasar da tafi yawan al'umma a yankin gabashin Afirka ke shirin fadawa, Abiy ya bayar da sanarwar cewa a shirye yake ya hau kan teburin tattauna matsalolin kasar, matakin da ake ganin ya kamata ya dauka tun bayan da ya zama firaminista shekaru ukun da suka gabata. Abin tambaya shi ne, ko za a yadda da kalaman firaministan da ke zaman cikakken mabiyin addinin Kirista, bayan jerin karairayi da gwamnatin tai ta yi kan halin da ake ciki a yankin Tigray a baya-bayan nan. In har 'yan tawayen na People's Liberation Front in Tigray (TPLF) suka samu dama, to za a iya cewa kwanakin Abiy kan karagar mulki a kirge suke.