1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus akan nahiyar Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 31, 2025

Ta'asar mayakan sa kai na RSF a yankin el-Fasher a Darfur na kasar Sudan ya dauki hankalin Jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/52vNU
Wasu sojojin rundunar sa kai ta RSF yayin da suka isa wata kasuwa a gundumar Lalalah
Wasu sojojin rundunar sa kai ta RSFHoto: AP Photo/picture alliance

jaridar die Tageszeitung da ta mayar da hankali kan rahoton kisan mutane fiye da 460 marasa lafiya da mayakan RSF da ke rikici da sojojin gwamnatin Sudan suka yi a asibiti, bayan karbe iko da garin El Fasher. Jaridar ta ce: Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da kungiyoyin da suke ayyuka a yankin, sun tabbatar da abin da ya faru. Tuni Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci kawo karshen duk wani matakin kai farmaki a wuraren kula da lafiya a kasar ta Sudan, yayin da kasashen duniya ke bukatar ganin an hukuntan wadanda suke da hannu kan wannan hari.

Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan
Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan Hoto: Picture Alliance/Reuters

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta mayar hankali kan zaben Tanzaniya da aka gudanar ranar 29 ga watan Oktoba, inda Shugaba Samia Suluhu Hassan take neman sabon wa'adi. Jagoran adawa Tundu Lissu na garkame, a kan zargin laifukan cin-amanar kasa. Tashin hankali kan tsangwama da 'yan adawa ke fuskanta, ya mamaye kasar da ke yankin gabashin Afirka da al'uumarta kimanin milyan 37 suka cancanci kada kuri'a. Akwai fatan samun sauye-sauye da gudanar da zabuka masu inganci, yayin da Shugaba Suluhu Hassan ta karbi madafun iko bayan mutuwar Shugaba John Magafuli. Sai dai ana ganin, shugabar ta nuna ta fi kowa iya mulkin kama-karya da nuna rashin sanin ya kamata.

Zanga zangar matasa a Douala Kamaru bayan zaben shugaban kasa
Zanga zangar matasa a Douala Kamaru bayan zaben shugaban kasaHoto: Zohra Bensemra/REUTERS

A nata sharhin jaridar Zeit Online ta yi tsokaci ne kan yadda Shugaba Paul Biya na Kamaru ya sake lashe zabe a wa'adi na takwas, inda shugaban mai shekaru 92 a duniya yake fuskantar zanga-zanga daga 'yan kasar bayan an bayyana sakamakon zaben.  Kotun tsarin mulkin kasar ta sanar da cewa, Biya ya lashe zaben na ranar 12 ga watan Oktoba da kaso 53 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Shi kuwa Issa Tchiroma Bakary da ya kasance babban jagoran adawar kasar a zaben na bana, ya samu kaso 35 cikin 100.

Biya ya dauki madafun ikon kasar ta Kamaru a shekarar 1982 kuma tun lokacin yake sauya dokokin kasar yadda ya ga dama, inda ya soke wa'adin da mutum zai iya yi kan karagar mulki. A lokacin da zai kammala wannan wa'adin na takwas na tsawon wasu shekaru bakwai, zai kasance yana da kusan shekaru 100 a duniya. A hannu guda kuma, tuni jagoran adawa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.

Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara
Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara Hoto: Luc Gnago/REUTERS

Za mu karkare da jaridar die Tageszeitung a sharhinta mai taken: "Sunan tsoho da sabon shugaban kasa Ouattara. A Côte d'Ivoire Shugaba Alassane Ouattara ya sake zama shugaban kasa da kusan kaso 90 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Wannan ne wa'adi na hudu da ake ayyana shugaban mai shekaru 83, a matsayin shugaban kasa." Jaridar ta ce: Sakamakon zaben da shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasa CEI Ibrahim Kuibiert Coulibaly ya bayyana, bai zo da mamaki ba. Tun daga shekara ta 2011 ne dai, Alassane Ouattara ya dare madafun iko a Côte d'Ivoire.

A yanzu zai jagoranci kasar da ke yankin yammacin Afirka a karo na hudu, bayan da sakamakon zaben ya bayyana shi da wanda ya yi nasara da sama kaso 89 na kuri'un da aka kada a ranar 25 ga watan Oktoba. Jam'iyyar RHDP mai mulki a Côte d'Ivoire ta bayyana zaben da, "zaben raba-gardama mai matukar tarihi!" da ta ce al'ummar kasar sun zabi dorewar ci-gaba. Jean-Louis Billon ne yake mara masa baya da sama da kaso uku kacal na kuri'un da aka kada. Kaso 50 cikin 100 kacal cikin al'ummar kasar miliyan takwas da dubu 700 da suka cancanci kada kuri'a ne dai, suka fito rumfunan zabe.))