1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Tsugune ba ta kare ba a Sudan ga masu zanga-zanga

June 4, 2019

A yanzu masu zanga-zangar ta tsawon wata guda a kasar Sudan na cin gajiyar goyon baya daga kasashen Turai, a cewar Rainer Sollich na sashen Larabci na tashar DW cikin sharhinsa da ya rubuta.

https://p.dw.com/p/3Jq81
BG Sudan Proteste
Hoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

 

Tsawon wata guda aka kwashe ana gudanara da zangar-zangar cikin lumana da kwanciyar hankali. Sai dai kwatsam ta rikide zuwa tashin hankali sakamakon farawa masu zanga-zangar da jami'an tsaro suka yi. Harbin kan mai uwa da wabin da sojojin suka yi kan masu zanga-zangar ya janyo asarar rayuka tare kuma da jikkata wasu da dama. Tuni dai masu zanga-zangar suka janye daga yarjejeniyar da suka kulla da sojojin. Masu zanga-zangar da kuma jagororin adawar kasar ta sudan na son a kafa gwamnatin rikon kwarya da ta kunshi fararen hula masu yawa kuma ta hanyar dimukuradiyya, yayin da a hannu guda sojojin ke son yin shigege ta hanyar kankane komai da ya shafi gwamnatin rikon kwaryar.

Sollich Rainer Kommentarbild App

Tilas bangarorin biyu su yi taka tsan-tsan tare da gujewa duk wani mataki na kara tayar da tarzoma. Babu wanda zai ji dadin abubuwa su tabarbare bayan samun nasarar kifar da gwamnatin tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar Omar al-Baschir cikin kwanciyar hankali, cikin watan Afirilun da ya gabata. Sudan ta kasance cikin kasashe 20 da suka fi talauci a duniya musamman bayan ficewar Sudan ta Kudu daga kasar  cikin shekara ta 2011. Sai dai abin da ya kara tabarbara al'amuran kasar shi ne: Facaka da tattalin arzikin kasar da kuma cin hanci da rashawa. Kara farashin kudin burodi a karshen shekarar da ta gabata, shi ne ya janyo zanga-zangar da ta samun goyon baya daga masu matasakaicin karfi, inda daga bisani ta samu goyon bayan dinbin fararen hula. Ra'ayoyi sun banbanta tsakanin bangaren sojojin da na masu zanga-zanga. Kowa yana da tsa manufar da yake karewa, abin da iya janyo kara tabarbarewar al'amura har ma a gaza shawo kan matsalar. Duk wani mataki na tunzuri ka iya janyo hargitsi, hakn ce ta sanya masu zanga-zangar a Sudan da har kwo yanzu suke ci gaba da kiran a gudanar da zanga-zangar cikin lumana, ke samun goyon bayan da ya dace da wanda bai dace ba, har ma daga kasashen Turai.

BG Sudan Proteste
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Koda yake akwai wasu manyan bangarori a yankin da ke makwabtaka da Sudan din da baa sa fatan a samu nasarar cimma sahihin tsarin dimukuradiyya, musamman masarautar Saudiyya da ta Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Masar. Baki daya kasashen uku na da alaka ga wadanda suka fara kirkirar abin da ake kira da wai "Juyin-juya Halin Kasashen Larabawa", baki dayan mahukuntan kasashen uku na marawa sojojin Sudan baya, wadanda ake bukatar su a yakin da Saudiyya ke jagoranta a Yemen. Shugabannin kasashen uku, dukkansu ba sa fatan a samu nasarar samar da sahihiyar dimukuradiyya a Sudan, kasancewar hakan ka iya karfafa gwiwar 'yan adawa a kasashensu. Misali a Masar, a shekara ta 2014 an kashe daruruwan mutane a yayin kisan kiyashi a Rabaa, a wani mataki na hambarar da gwamnatin 'yan uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood da kuma dakile duk wani yunkuri na cimma kafa gawamnatin dimukuradiyya a yankin. Shugabannin kasashen uku na zaman shugabannin kama karya na hakika da aka taba gani. Tilas a kare yiwuwar faruwar irin haka a Sudan ta kowace hanya.