Sharhi: Mafita ga dambarwar zabe a Najeriya | Siyasa | DW | 17.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi: Mafita ga dambarwar zabe a Najeriya

Bayan da gwamnatin Najeriya ta amince da shawarwarrin da Kungiyar Tarayyar Turai ta bayar kan hanyoyin inganta zabe, akwai bukatar yin tankade da rairaya a duk lamuran da suka shafi zabe domin ya karbu a cewar sharhin.

 Shekaru da dama aka shafe ana kwan-gaba kwan-baya a harkokin zabe a tarayyar Najeriya duk da kasancewarta uwa maba da mama a fannin tattalin arziki da yawan al'umma. Kusan ma gara jiya da yau a ke yi a duk lokacin da aka shirya zabe, inda zabukan farko da aka gudanar bisa tafarkin dimukaradiyya ke fin na gaba inganci. Wannan dai ba ya rasa nasaba da buris da irin shawarwarin da ake ba su na kawo gyara ga zaben ba, sai dai a karon farko tun bayan da Najeriya ta koma kan tafarkin dimukaradiyya shekaru 20 da suka gabata, gwamnatin da ke mulki ta karbi shawarwarin da Kungiyar Gamayyar Turai ta bayar kan al'amuran zabe da hannu bi-biyu, tare da alkawarin aiwatar da su a ciki lokaci. Hasali ma dai munin da zaben baya-bayannan ya yi, ya sa kungiyar EU ta bayyana kura-kurai 30 da aka tabka a zabukan shugaban kasa da na gwamnoni da ma na 'yan majalisun dokoki na 2019, lamarin da ke nuna cewa matsalolin da aka ci karo da su sun ninka na zabukan baya.

Rashin bin shawarwari ya cilasta dage zabe a Najeriya

Najeriya dama ta gaza aiwatar da sauye-sauyen da aka alkawarta a zaben da ya gabata na 2015 na yi wa wasu dokokin zabe gyaran fuska domin 'yan kasa su samu sukunin kada kuri'a cikin 'yancin da walwala, sannan zaben ya samu karbuwa a ciki da wajen Najeriya. Maimakon haka sai aka yi kisto a kan kwarkata, ma'ana aka ci gaba da dora duk lamuran zabe a kan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC duk da irin kalubale da ta fuskanta a baya, lamarin da ya cilasta ta sake dage zabe na tsawon kwanaki. Sannan kamar yadda aka saba wasu daga masu rike da manyan mukamai, gwamnoni ga misali sun ci gaba da amfani da hanyoyi da dimukaradiyya ba ta amince ba, kamar amfani da kudi zuwa ga daban siyasa wajen tursasa wa masu zabe, tare da cin zarafin 'yan jarida da turawan zabe saboda kawai su cimma burinsu na siyasa.

Akwai bukatar raba dan duma da kabewa a harkokin tsara zabe

To ba girin-girin ba dai ta yi mai, kasancewa ba za a iya daukar matakan inganta zabe a Najeriya ba matukar ba a dubin lokaci tare da tuntubar dukkanin bangarori dabam-dabam domin zama kan teburi guda ba. Tabbas akwai bukatar raba dan duma da kabewa a harkokin tsara zabe. Ma'ana a dauke wani bangare daga hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC musamman ma game da batun rijistar jam'iyyun siyasa da tantance 'yan takarar da suka cuka ka'idoji. Maimakon haka ta maida hankali kacokan kan tsara zabe kama daga samar da kayan kada kuri'a zuwa rarrabasu a mazabu, da kuma tattara sakamako a cikin yanayi mai kyau tare da sanar da wanda Allah ya nufa da arziki. Su kuwa 'yan takara da ke tursasa wa masu zabe ko yin aringizon kuri'u, a tanadi hukunci mai tsanani kansu na hanasu tsayawa takara na wani lokaci idan aka samesu da aikata wannan laifi, tare da kare rayuka da lafiyar masu kada kuri'a a duk inda suka kasance, wadanda rashin fitowarsu ke rage wa dimukaradiyyar Najeriya armashi. Ita kuwa gwamnati da ke kan karagar mulki, tilas ne ta tabbatar da cewa abin da talakawa suka zaba shi a ka basu, ko da kuwa ya kasance abokan hamayya suka zaba. Yayin da ita kuma kotun zabe da ke zaman mafaka ta karshe ta tabbatar da dimukaradiyya da adalci, ta zama mai tabbatar da adalcin maimakon bai wa wanda ya shigar da kara gaskiya ba tare da zurfafa bincike ba. sannan a dauki matakan rage lokacin da ake diba da hanyoyin da ake bi wajen tabbatar da wanda ya lashe zaben. Idan ba haka za a ci gaba da yi ba, to ba zabi a harkokin zaben tarayyar Najeriya.