Sharhi: Kyakkyawan fata na Obama | Siyasa | DW | 11.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi: Kyakkyawan fata na Obama

Shugaban Amirka Barack Obama ya yi jawabinsa na bankwana ga al'ummar kasar. Wannan jawabi ne da tarihi ba zai taba mantawa da shi ba, inji wakilin DW a Washington Miodrag Soric a cikin wannan sharhi da ya rubuta.

Miodrag Soric ya ce al'adar yin jawabi na bankwana ga shugaban kasa a Amirka ya samo asali ne daga shugaban kasar na farko wato George Washington. Ana yin irin wannan jawabi saboda dalilai guda biyu inda ake duba irin abubuwan da aka cimma a baya sannan a yi hange na irin abinda zai faru nan gaba musamman ma kalubalen da kasar da kuma shugaba ma jiran gado zai iya fuskanta. Jama'a ba su fiya damuwa da tuna galibin irin wadannan jawabai da shugabanni masu barin gado kan yi ba don kuwa wasunsu na cike ne da kalamai na zuga kai ko kuma kare kai ko bada karin dalilai na daukar wasu matakai lokacin da shugaba ke rike da madafun iko.

Soric Miodrag Kommentarbild App

Miodrag Soric da ke shugabantar ofishin tashar DW a Washington

Guda daga cikin irin wadannan jawabai da za a iya cewar sun yi fice kuma ba za a manta da su ba shi ne wanda Dwight Eisenhower ya yi, inda a ciki ya yi gargadi game da batun da ya danganci harka ta soji. Wani jawabi da za a iya cewar ya kasance kan godabe guda da na Eisenhower shi ne wanda Barack Obama ya yi wanda ke cike da ban tausayi da kuma cikakken fata wanda da dama daga cikin al'ummar kasar suka yi mamakinsa saboda wasu abubuwan da ya ambata a cikin jawabin nasa ba su da banbanci sosai daga irin abubuwan da magajinsa wato Donald Trump wanda ya sha alwashin kawar da wasu abubuwan da gwamnatin kasar ta yi a shekaru takwas din da suka gabata.

Shugaban da bashi da wata badakala

To sai dai wannan mataki da Trump din ya sha alwashin dauka bai girgiza shi ba kuma bai sanya ya karaya ba don kuwa ya yi hasashen faruwar hakan kana a share guda ya sake jaddada irin amincewar da ya yi wa al'ummar Amirka da ma kundin tsarin mulkin kasar har ma a jawabin nasa na Chicago ya ke cewar demokradiyyar kasar za ta iya kasancewa ne kawai cikin mawuyacin hali idan 'yan kasar suka yi mata rikon sakainar kashi. Jawabin na Obama dai ya nuna cewar shi dattijo ne mai kamala da kima da kuma sanin ya kamata wanda a iya cewar iya ya tsawon mulkinsa ba wata badakala ko abin kunya da ya taso, sabanin wanda zai gada wanda tuni kafafen watsa labarai da shafukan jaridu suka cika da irin abubuwan kunya da suka taso tun ma bai hau kan gadon mulki ba.

Obama ka iya yin alfahari da kansa

A jawabin nasa na bankwana, an jiyo Obama na lissafa irin abubuwan da ya cimma ciki kuwa har da ceto tattalin arzikin kasar a 2009 da rage yawan marasa aikin yi da shirin nan na kiwon lafiya da aka yi wa lakabi da Obamacare da hukuntan Bin Laden da sabbin manufofi na alkinta muhalli gami da cimma matsaya kan dangantakar Iran da kasar da maido da hulda da kasar Cuba. Wannan nasarori sun samu ne duk kuwa da irin yadda 'yan jam'iyyar adawa ta Republican suka rika cin dunduniyarsa. Irin wadannan nasarori da aka cimma sun sanya Amirka ta samu cigaba fiye da yadda take shekaru takwas din da suka gabata, don haka dole ne ya yi alfahari da abubuwan da ya cimma.

Amma kuma duk da wadannan nasarori akwai abubuwan da za a iya cewa ba a cimma ba a shekaru takwas na Obama, ciki kuwa har da wagegen gibin da ke akwai tsakanin masu kudi da talakawa da batu na nuna wariyar launin fata duk kuwa da cewar bakar fata ne ke jagorantar kasar. Obama dai bai so a ce a batun banbancin launin fata ya kasance wani abu da zai mamaye shekarun mulkinsa ba. Sai dai kamar yadda ya fadi, canji ba abu ne da ke faruwa cikin hanzari ba, kuma wannan abu ne da aka gani tun a kwanakin farko na hawansa mulki. Amirkawa da dama dai sun fara kewar Obama tun ma bai kai ga barin gadon mulki ba.

Sauti da bidiyo akan labarin