Sharhi: Bayan kisan malami a Faransa | Siyasa | DW | 27.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi: Bayan kisan malami a Faransa

'Yan darikar Katolika sun shiga azumi da addu'o'i sakamakon hare-hare na ta'addanci da suke fuskanta, inda a hannu guda mabiya darikar ta Katolika ke ci gaba da juyayin kisan wani malamin coci a Faransa.

Malamin mai suna Jacques Hamel ya riski ajalinsa ne ya na da shekaru 85 a duniya, wanda kuma kisan nasa ya tada hankalin jama'a a sassan duniya daban-daban kana kuma akewa kisan kallon yin karan tsaye ga wuraren ibada da ma sauran wurare masu tsarki duba da cewa an hallaka shi ne a cikin Coci a wani kauye da ke Faransa. Kisan dai wanda aka danganta da kisa irin na dabbanci abu ne da ya girgiza Faransa, duk kuwa da cewar kasa ce da ba ruwanta da addini, darikar Katolika na da dadadden tarihi a wannan kasa. Shi dai Hamel da aka hallaka shi a cocin Saint-Etienne-du-Rouvray ya shafe tsahon shekaru 58 a matsayinsa na Fada. Duk kuwa da cewar ya yi ritaya kimanin shekaru goma da suka wuce, ya kan jagoranci mutane wajen yin ibada a wannan cocin.

Ginin cocin Saint-Etienne-du-Rouvray da ke Faransa

Ginin cocin Saint-Etienne-du-Rouvray da ke Faransa

Mabiyansa dai sun yi masa shaidar kasancewa mutumin kirki wanda ke haba-haba da jama'a, kuma hakan ya sanya al'umma na kaunarsa. Hamel dai mutum ne da bai tara abin duniya ba kamar sauran takwarorinsa da ke Faransa. Malamin cocin dai ya gamu da ajalinsa ne lokacin da wasu 'yan ta'adda suka bukaci ya tsuguna a kasa bayan da suka shiga cocin da ya ke ciki, a kokarinsa na kare kansa ne maharan suka yi masa yankan rago a dai-dai wurin da masu ibada a cocin ke yin sujjada. Tuni dai mayakan kungiyar 'yan ta'addan IS suka sauya ma'anar mutuwa ta shahada ko kuma mutuwar da mutun zai yi ya shige aljanna kai tsaye.

Mutuwar da ta girgiza kowa

Fada Jacques Hamel dai ya rasa ransa a lokacin da yake kan aiki na ibada kuma wannan lamari ya girgiza 'yan Faransa ciki kuwa har da Archbishop na Rouen Dominique Lebrun wanda ya samu wannan labarin lokacin da ya ke wajen taron ranar matasa ta duniya a birnin Krakow na kasar Poland, to sai dai duk da kaduwar da ya yi, Lebrun ya ce ya yi imanin cewar ba wani makami da 'yan darikar ta Katolika ke da shi wanda ya fi addu'a da kuma kaunar juna ko 'yan uwantaka. Wannan ne ma ya sanya mabiya darikar ta Katolika a Faransa suka ware ranar Laraba 27 ga watan Yulin da muke ciki domin yin azumi da addu'o'i sakamakon wannan ibtila'i da suka gamu da shi.

Taron malaman addinai da shugaban kasar Faransa François Hollande.

Taron malaman addinai da shugaban kasar Faransa François Hollande.

Malaman addinin Kirista ciki kuwa har da shugaban kungiyar bishof-bishof da ke nan Jamus wato Reinhard Marx sun bukaci mabiyansu da su guji maida martani ko daukar fansa sakamakon kisan na Fada, inda a bangare guda kuma ya ce kisan da aka yi a Saint-Etienne-du-Rouvray wani tafarki ne na nuna kyama ko tsana amma kuma zasu yi kokarin kawar da kansu daga hakan kuma dole a yi dukkannin mai yiwuwa wajen kawo karshen wannan lamari da ka iya haifar da tashin hankali.

Mataki daga Saudiya da Wahabiyawa

Ayar tamabaya dai a nan ita ce shin me ya sanya zuciyar wanda suka yi kisan ke cike da kyama? Shin ta ya za a fahimci tsarin kungiyar IS da ba abinda ta sanya gaba sai zubar da jini? Wannan tsari nasu abu ne da ke da saurin harzuka mutum amma a gefe guda Musulmi a nan Jamus na yin Allah wadai da irin kisan da 'yan kungiyar ke yi kuma ma tuni suka nuna rashin jin dadinsu da kisan da aka yi wa Fada Hamel. Yanzu haka dai lokaci ya yi da Saudiyya za ta dau mataki, haka ma abin ya ke ga wanda ke bin tafarkin wahabiyawa. Shin ma wannan hare-haren ta'addancin na girgiza su kuwa? Shin hudubobin da ake a masallatai da makarantu na nuna cewar kisan da irin wadannan maharan ke yi ya sabawa koyarwar addinin Islama? Akwai da dama da ke yin hakan kuma ba su da wata alamar dainawa.

Sauti da bidiyo akan labarin