Sharhi akan harin Iraki | Siyasa | DW | 23.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sharhi akan harin Iraki

Rikici ya zama ruwan dare a Iraki sakamakon hari a Samarra in ji Peter Philipp a cikin sharhinsa

Harin akan gidan ibadan na ‘yan shi’a ba kome ba ne illa tsabar ta’addanci. Domin kuwa ba kawai saboda barnatar da gidan ibadan ne aka kai wannan hari ba. Masu alhakin wannan danyyen aiki sun sani cewar duk wani harin da za a kai kan wata kafa mai tsarki zai ta da hankalin ‘yan shi’a ya kuma harzuka su kuma ga alamu wannan shi ne ainifin makasudin wannan mummunan mataki na Allah waddai domin ta da zaune tsaye ba gaira ba dalili, ba ma kawai tsakanin ‘yan Shi’a ba har ma da ‘yan Sunni, wadanda ake kirarin cewar wai su ne suka kai harin. ‘Yan ta’adda sune suka saba bin irin wannan manufa. Gargadi da shugaban kasar Iraki Jalal Talibani yayi a game da fuskantar wani mummunan yanayi na yakin basasa, ba neman wuce gona da iri ba ne. Domin kuwa manufar harin shi ne a yi cikas ga duk wani matakin da zai kai ga samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Iraki da kuma ci gaba da haddasa baraka tsakanin ‘yan Shi’a da ‘yan Sunni. A irin wannan hali manyan malamai na addini sune zasu iya taka muhimmiyar rawa domin hana dakatar da yamutsin da ake neman ganin ya samu. Misali Ayatullah Ali Assistani wanda ‘yan Shi’a ke biyayya ga maganarsa sau da kafa, wanda kuma tun da farkon fari yayi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan afkuwar wannan danyyen aiki. In har wannan kira ya cimma nasara to kuwa ba shakka za a samu kafar dakatar da barakar dake dada karuwa tsakanin ‘yan Shi’a da ‘yan Sunni a kasar Iraki. Kasar ta dade tana mai bin tsarin siyasar da ba ya da hulda da al’amuran addini. Sake komawa akan wannan tafarki zai taimaka mata ainun wajen karya alkadarin wasu rukunoni na kasar dake neman amfani da addini domin cimma bukatunsu na duniya. Dangane da kasashen ketare kuwa, musamman ma na nahiyar Turai ka da su yi zaton cewar abubuwan dake faruwa a Iraki lamari ne da ya shafi Musulmi su ya su kamar yadda wasu suka rika ikirarin dangane da zanen batancin nan akan Annabi mai tsira da aminci. A saboda haka ba ma zai zama abin mamaki ba idan an fuskanci irin wannan farmaki kan babbar mujami’ar nan ta kolon. Ka da fa a manta da abin da ya faru a kasar Netherlands kwanan baya inda a cikin kiftawa da Bisimillah aka rika kone masallatai sakamakon kisan gillar da aka yi wa wani dan kasar mai shirya finafinai da ake kira van Gogh.