Shan magani a boye wa binciken Ebola | Labarai | DW | 03.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shan magani a boye wa binciken Ebola

Yanayin zafin jikin mutum shi kadai ba ya wadatarwa a gane mutum na da cutar Ebola akwai bukatar a matsa bincike.

Mutane da suka harbu da kwayoyin cutar Ebola daga kasashen yammacin Afrika na amfani da kwayoyin Ibroprofen, da ma bada wasu bayanai na karya idan suna son shiga jiragen sama, kamar yadda wasu kwararru a fannin lafiya da su ke neman matsa bincike dan gano matafiya da ke dauke da cutar suka shedar

Suka ce akalla matafiyan daga kasashen da wannan cuta tafi yi wa illa ana duba yanayin zafin jikin mara lafiya ne kawai, wanda shi ne abinda ake yi a filin tashi da saukar jiragen sama na kasashen Laberiya da Guinea da Saliyo, hakan kuma ba zai wadatarba.

A cewar Sean Kaufman wanda ya kasance kwararre kuma shugaban wata cibiya da ke gudanar da bincike a wannan fannin a Atlanta na Amurka ya ce na'urorin da ake amfani da su wajen gwajin yanayin zafin jikin dan adam karfin su kan ragu, kuma a irin wannan lokaci ba lalle su rika bada sakamako sahihi ba.