Senegal: Kokarin magance rikicin Casamance | Labarai | DW | 19.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Senegal: Kokarin magance rikicin Casamance

Hukumomin tsaro a kasar Senegal sun gabatar da mutane 16 daga cikin 22 da aka kama a gaban kotu, bayan kisan wasu mutane 14 da aka yi masu saran itace a dajin Casamance da ke Kudancin kasar.

Tschad Gericht in Dakar Hissene Habre Prozess

Babban gidan shari'a na birnin Dakar a Senegal

A ranar 14 ga wannan wata na Janairu ne dai jami'an tsaron jandarmomi na kasar ta Senegal suka kama mutane 22 da ake zargi da hannu a kisan mutanen14 da aka yi na ranar shida ga wata a cikin gandun daji nan na Bayotte da ke kusa da Ziguinchor babban birnin yankin, wanda ke da iyaka da Gambiya ta bangaran Arewa da kuma kasar Gini Bissau ta bangaran Kudu.

Mutanen 16 an mika su ne a hannun kotu inda ake inda ake tuhumarsu da laifin kisan kai da kuma tayar da zaune tsaye.

Shugaban kasar ta Senegal Maky Sall ya bada umarni ga gwamnati da ta aiwatar da cikakken bincike don gano gaskiyar wannan lamari ta yadda za a gurfanar da duk wani mai hannu ciki.