Scotland za ta ci gaba da zama a Birtaniya | Labarai | DW | 19.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Scotland za ta ci gaba da zama a Birtaniya

Sakamakon da ke fitowa daga yanki Scotland na Birtaniya na nuna cewar mafi akasarin al'ummar yankin sun zabi ci gaba da zama tare da Birtaniya.

Duk da cewar galibin al'ummar da ke biranen Dundee da Glasgow sun nemi a balle, sakamakon da aka tattara ya zuwa yanzu ya nuna cewar kashi 55 cikin 100 na al'ummar yankin ne suka amince da cigaba da zama a tare da Birtaniya yayin da kashi 45 suka nemi a balle. Fitar sakamakon ke da wuya sai masu rajin ganin an ci gaba da zama tare da Burtaniya suka barke da sowa da tafi na murna.

Tuni dai Alex Salmond da ke kan gaba wajen ganin an balle daga Birtaniya ya amince da shan kaye a wannan fafutuka da suka kwashe tsawon shekaru suna yi, sai dai ya nemi London ta cika alkawarinta na bai wa yankin damar samun karin karfin iko.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Suleiman Babayo