1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin shugabanci a Yukrain

Usman ShehuFebruary 23, 2014

'Yan majalisar dokokin Yukrain sun amince da naɗin Oleksandr Turchynov, a matsayin sabon shugaba ƙasa, wanda kafin naɗinsa shi ne shugaban majalisar dokoki ƙasar

https://p.dw.com/p/1BECw
Ukraine Krise Alexander Turtschinow 22.02.2014 2013
Oleksandr TurchynovHoto: Reuters

Bayan tsoma bakin da majalisar dokokin ƙasar Yukrain ta yi, inda ta maido da kundin tsarin mulki, kana ta tsige Viktor Yanukovych a matsayin shugaban ƙasa, majalisar daga bisani ta naɗa shugaban majalisar dokoki a matsayin shugaban kasa na wucin gadi. An dai ɗau wannan matakinnne bayan kwashe watanni ana zanga-zanga.

Sabon shugaban da aka naɗa dai yana da alaka da tsohuwar Firaministar Yulia Tymoshenko, wanda kuma tuni aka sako ta daga gidan kaso. Jim kaɗan bayan fitowarTymoshenko, ta yi wa dubban magoya bayanta da suka hallara a Kiev babban birnin kasar jawabi. Daga bisa ni ta kuma yi magana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta wayar tarho. Inda Merkel ta buƙaci Tymoshenko da ta himmatu wajen haɗa kan ƙasar ta Yukrain. Ga abinda ta tsohuwar firaministar ta fadawa magoya bayanta.

Ukraine Julia Timoschenko Rede Maidan 22. Feb. 2014
Yulia TymoshenkoHoto: Getty Images

Ta ce, "mu yi waƙa wa 'yan ƙasar Yukrain. Wadanda suka yi gaba da gaba da harsashen bindiga na jami'an tsaro. Dukkanmu muna haɗe tsuntsiya daya, kuma a yanzu muna murna. A yanzu muna da babban aiki da ke gabanmu, wato na tabbatar da jinin mutanenmu bai zuba a banza ba. Dole dukkan 'yan ƙasarmu, mu tabbatar basu yi asaran sadaukar da rayukansu da suka yi ba. Wannan kuma shi ne duk wanda ke da mutunci ya yi yaƙi a kansa. Na yi imani da Yukrain"

Tuni dai ƙasashen duniya suka fara mai da martani, bayan matakin da majalisar dokokin ƙasar ta Yukrain ta ɗauka, na kawar da Viktor Yanukovych da naɗa wanda zai maye gurbinsa. Inda a taron da suke gudanarwar ƙasashe 20 da sukafi ƙarfin tattalin arzikin masana'antu a duniya wato 'yan ƙungiyar G20, suka yi alƙawarin tallafawa ƙasar ta Yukrain domin farfaɗowa. Kamar yadda aka jiyo shugabar asusun bada lamuni ta duniya wato IMF Christine Lagarde na cewa.

Ukraine Viktor Janukowitsch Porträt ARCHIV
Viktor YanukovychHoto: picture-alliance/dpa

"Walau dai shawara ta ɓangaren tsaren-tsaren siyasa, ko kuma na kuɗi da garanbawul na tattalin arziki, duk waɗannan muna shirye mu yi hakan"

A martaninsa ministan harkokin wajen ƙasar Bitaniya William Hague, cewa ya yi, har yanzu ba za a ce Yukrain ta fita cikin rigimar siyasa ba, domin kuwa su ma kansu 'yan adawa suna da bambancin ra'ayi tsakaninsu. Don hanka sauke Viktor Yanukovych daga mulki, ba ƙarshen labarin bane. Kana Hague ya ce dole ƙasashen Turai su yi aiki tare da Rasha, a duk matakin sasanta siyasar Yukrain.

Tuni dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta yi magana da shugaban ƙasar ta Rasha Vladimir Putin, kan makomar ƙasar ta Yukrain. Inda yanzu haka aka tsara gudanar da sabon zaɓe a watan Mayu dake tafe a bana.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdourrahmane Hassane