Sauraron shari´ar Jacob Zuma kan cin hanci da rashawa | Labarai | DW | 05.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sauraron shari´ar Jacob Zuma kan cin hanci da rashawa

A yaune ake fara sauraron shari´ar tsohon mataimakin shugaban kasar Africa ta kudu, wato Mr Jacob Zuma, bisa tuhumar cin hanci da rashawa.

Mr Zuma a cewar bayanai, zai fuskanci tuhuma ne akan cin hanci da rashawar daya shafi wata yarjejeniyar sayen makamai ta biliyoyin daloli da aka sawa hannu a shekara ta 1999.

Ya zuwa yanzu dai tuni dubbannin magoya bayan tsohon shugaban suka fara hallara a Peter Marisbug, domin sauraron wannan shari´a.

Idan dai an iya tunawa, a shekarar data gabata ne Mr Thabo Mbeki ya kori Mr Jacob Zuma daga mukamin sa na mukkaddashin mataimakin shugabasn kasa, to amma har yanzu shine mataimakin shugaban jam´iyyar ANC mai mulkin kasar.

A waje daya kuma, Shugaban kasar Russia Mr Vladimir Putin an shirya cewa zai soma wata ziyarar aiki izuwa kasar ta Africa ta kudu, ziyarar daya zuwa yanzu ake kallon ta, a matsayin wata kafa da Russia zata jaddada fada ajin ta a yankin.

A lokacin ziyarar ana sa ran shugabannin biyu, zasu rattaba hannu kann yarjeniyoyi da suka shafi kasuwanci da kuma saka jari. Kana a hannu daya kuma ana kyautata zaton cewa Mr Putin da Mr Thabo Mbeki zasu tattauna matsaloli na yankin gabas ta tsakiya da kuma rikicin makamin nukiliyar kasar Iran.