A cikin shirin za a ji kungiyar kare hakkin dan Adam Amnesty International a wani sabon rahoto da ta fitar, ta zargi sojojin Najeriya da cin zarafin da azabtar da matan da suka gujewa rikicin Boko Haram da kuma ke zaune a sansanin yan gudun hijira ta hanyar yi musu fyade.