Saudiya za ta yi amfani da sojojin kasa a rikicin Yemen | Labarai | DW | 21.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiya za ta yi amfani da sojojin kasa a rikicin Yemen

Saudiya za ta yi amfani da sojojin kasa a rikicin Yemen yayin da rikcin kasar ta Yemen rincabewa

Sarki Salman na kasar Saudiya ya ba da umurnin wa dakarun musamman su shirya domin kai farmaki ta kasa kan mayakan 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito. Kasar ta Saudiya ke jagatantar hare-hare ta sama da ake kai wa kan mayakan na 'yan tawayen Houthi.

Kawo yanzu babu wani tabbaci kan lokacin da dakarun na Saudiya za su kutsa cikin kasar ta Yemen, da yadda za su shiga cikin rikicin.

Mayakan na Houthi da ke saman tallafin kasar Iran suna fafatawa da dakarun da ke biyayya wa Shugaba Abd Rabu Mansour Hadi na kasar Yemen, abin da ya yi sanadiyar hallaka mutane masu yawa, yayin da wasu daruruwa suka samu raunika.