Saudiya tana kara samun makamai kan yakin Yemen | Labarai | DW | 08.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiya tana kara samun makamai kan yakin Yemen

Amirka ta kara zimma na bai wa Saudiya makamai kan rikicin kasar Yemen

Amirka ta kara zimma wajen bai wa kasar Saudiya makamai yayin da take jagoranci kai hare-hare kan mayakan Houthi na kasar Yemen wadanda suke samun tallafi daga kasar Iran.

Saudiya tana ci gaba da barin wuta ta sama inda take iko da sararin samaniyar kasar ta Yemen, domin kare gwamnatin Shugaba Abd Rabbo Mansour Hadi, wadda ke fuskantar tawaye daga mayakan na Houthi. Daruruwan mutane sun mutu yayin da wasu dubbai suka jikata sakamakon rikicin da ke faruwa.

Mayakan 'yan tawayen na Houthi sun kame yanki girma a cikin kasar ta Yemen, yayin da kungiyar ba da agaji ta Red Cross take nuna damuwa bisa yadda yakin ke ritsawa da fararen hula.