Saudiya na jibge makamai a Yemen | Labarai | DW | 24.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiya na jibge makamai a Yemen

Jirage sun fara isa Aden a karon farko tun bayan kwace iko da birnin da mayakan sa kai da ke goyon bayan Shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi na Yemen da tallafin sojojin Saudiya suka yi.

Rahotanni sun nunar da cewa daga bisani wasu jiragen na Saudiya guda biyu sun sauka a birnin na Aden a wannan Jumma'a da kayan aikin da ake bukata domin sake bude filin sauka da tashin jirgen saman na Aden yayin da jirgin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ya sauka da kayan agaji. A yanzu haka dai rundunar taron dangin da Saudiya ke jagoranta na ci gaba da yin barin bama-bamai a baban birnin kasar ta Yemen Sanaa da kuma wasu gundumomi a birnin na Aden da suka hadar da Dar Saad da Hael da kuma al Khadra kana suna kuma kai farmaki a gundumomin Marib da Shabwa da Abyan da Taiz da kuma Amran a kokarin da suke na kwace baki dayan yankunan da ke hannun 'yan tawayen Houthi.