1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiya ta karyata ikirarin Isra'ila na shiga kasar

Ramatu Garba Baba
January 27, 2020

Gwamnatin Saudiyya ta karyata batun da ke yawo na bai wa Yahudawan Isra'ila izinin shiga kasarta bayan da ministan harkokin cikin gidan kasar ya ce babu abinda ya sauya a dokokinsu na haramcin da aka sanyawa Isra'ilan.

https://p.dw.com/p/3Wt3j
Türkei Konsulat von Saudi-Arabien in Istanbul
Hoto: Getty Images/AFP/O. Kose

Dokar na nan daram inji mahukunta Saudiya saboda haka duk mai dauke da fasfon kasar ba zai sanya kafarsa a kasa mai tsarki ba. A jiya Lahadi ne ma'aikatar harkokin cikin gidan Isra'ilan, ta fidda sanarwar, inda a ciki ta ce an amince da bai wa 'yan kasar izinin shiga Saudiyya, walau don ibada ko hada-hadar kasuwanci na wani takaitaccen lokaci. 

Yanzu dai an kasa kunnuwa don jin sakamakon bayanan da Shugaban Amurka Donald Trump zai yi a game da shirin samar da zaman lafiya a tsakanin  Yahudawa da Falisdinawa a wannan Litinin, kafin a kai ga fahimtar yadda dangantaka a tsakanin Isra'ila da sauran kasashen musulmi za ta kasance.