Sarkozy ya yi gargaɗi ga ′yan Alƙa′ida | Labarai | DW | 26.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarkozy ya yi gargaɗi ga 'yan Alƙa'ida

Alƙa'ida ta ce ta kashe Bafaranshen ne domin ɗaukar fansan harin Sojojin Faransa da Murtaniya

default

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya tabatar da mutuwar Bafaranshen nan da ƙungiyar Al Qa'ida ta yi garkuwa da shi a arewacin Afirka.

A wani saƙon rediyo da shugaban ƙungiyar ta Al Qaida reshen ƙasashen Madgreb ya fitar ta gidan talabijin na AlJazeera, ya ce an kashe Bafaranshen ne a ranar Asabar domin ɗaukar fansan harin 'yan sandan Faransa da na Murtaniya suka kai akan 'ya'yan ƙungiyar.

Sarkozy ya ce yanzu haka ma dai ministan harkokin wajen Faransan Bernard Kouchner zai kai ziyara ƙasashen Niger da Mali da kuma Murtaniya da nufin tattauna matsalar tsaron Faransawa da ke yankin.

Sarkozy yayi gargaɗin cewar za'a ɗauki matakan ramuwar gayya akan waɗanda suka kashe Michel Germaneau, Bafaranshen ɗan shekaru 78.

Itama ƙungiyar AU na haɗa kan ƙasashen Afirka dake taro a kampalan Uganda tayi Allah wadai da kisan ɗan ƙasar ta faransan a Mali.

Ɗaya daga cikin batutuwan da shugabanin na Afirka ke tattaunawa dai sun haɗa da batun tabbatar da tsaro a yankin ƙasashen Afirka.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Muhammad Nasir Awal