Sarkozy na son shugabancin Faransa | Labarai | DW | 22.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarkozy na son shugabancin Faransa

A cewar majiyar kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP Sarkozy ya ce zai so ya jagoranci kasar duk da irin matsaloli da sarkakiyar da siyasar Faransa ke fiskanta

Frankreich ehemaliger Präsident Nicolas Sarkozy

Tsohon Shugaba Nicolas Sarkozy

Tshohon shugaban kasar ta Faransa Nicolas Sarkozy, a ranar Litinin din nan ya bayyana cewa zai nemi amincewar jam'iyyarsa dan ya fito a fafata da shi a takarar shugabancin kasar Faransa a zaben 2017.

A cewar majiyar kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP, Sarkozy da ya jagoranci kasar ta Faransa a tsakanin shekarun 2007 da 2012 ya ce zai so jagorantar kasar a shekaru biyar, duk kuwa da irin kalubale da kasar ke fiskanta, na da fata nagari a kanta.

Sarkozy dan shekaru 60 mai ra'ayin mazan jiya ba ya boye kwadayinsa dai na komawa kan karagar mulkin wannan kasa ta Faransa inda ya bayyana da cewa babban kalubalenta na zama yadda za su kare tsarin rayuwarsu ba tare da sun mai da kansu saniyar ware ba a tsakanin kasashen duniya.