Sanders ya yi mubaya′a ga Hillary Clinton | Labarai | DW | 26.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sanders ya yi mubaya'a ga Hillary Clinton

Bernie Sanders ya bayyana tsohuwar abokiyar hamayyarsa wato Hillary Clinton a matsayin wacce ta cancanci ta zamo shugabar kasar Amirka a nan gaba.

Bernie Sanders tsohon dan takarar neman shugabanci Amirka a karkashin inuwar jam'iyyar Democrate ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a yammacin jiya a birnin Philadephie a wurin babban taron kasa na jam'iyyar da zai kai ga kaddamar da Hillary Clinton a matsayin 'yar takarar jam'iyyar a zaben watan Nuwamba.

Sai dai da dama daga cikin magoya bayan Sanders din sun yi ta kuwar nuna rashin jin dadin kalaman nasa na yabo zuwa ga abokiyar hamayyar tasa. Abinda ke kasancewa wata alamar da ke nuni da cewar babu tabbas magoya bayansa su kada mata kuri'arsu a ranar zabe.