Sanarwar bayan taron G20 | Labarai | DW | 12.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sanarwar bayan taron G20

ƙasashen da suka fi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya sun sha alwashin kauce ma rage darajar takardar kuɗaɗensu.

default

Shugabanni a taron G20

Shugabannin ƙasashe 20 da suka fi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya sun kammala taron kwanaki biyu da suka gudanar a birnin Seoul na ƙasar Koreya ta kudu. Cikin sanarwar bayan taro da suka wallafa, ƙasashen sun amince da kauce ma rage darajar kuɗaɗe da wasunsu ke yi domin caɓa ƙazamar riba a hajojin da suke ƙerawa. Wannan matakin an ɗauke shi ne da nufin kawo ƙarshen zargen junansu da ƙasashen Amirka da China ke yi game da karyar darajar takardar kuɗinsu da suke yi domin cimma burinsu na cinikayya.

Taron ya kuma amince da wani sabon tsari da zai bayar da damar gwada mizanin koma bayan tattalin arzikin duniya, matakin da a cewar shugabanin zai sa a ɗauki matakan kauce wa jefa tattalin arzikin duniya cikin wani mawuyacin hali. Shugaba Barrack Obama na Amirka ya ce sun yi nasarar ɗora tattalin arzikin duniya kan kyakyawan turba sakamakon magance babance-babancen da ke tsakaninsu.

Shugaban ya kuma ce ƙasashen 20 sun kafa wani sabon tsari da ya tanadi tallafa wa ƙasashe masu tasowa domin su magance ƙarancin abincin da ke addabarsu. Hakazalika, ƙasashen da suka fi ƙarfin tattalin arziƙin sun yi alƙawarin bayar da gudun mawar da ta dace domin haƙa ta cimma ruwa a taron ɗumamar yanayi da zai gudana wata mai zuwa a birnin Cancun na ƙasar Mexico.

Mawallafi: Mouhamadou awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala