Samar da alawar Chocholate a Ghana | Himma dai Matasa | DW | 15.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Samar da alawar Chocholate a Ghana

Wasu 'yan mata a kasar Ghana sun hada hannu da nufin bunkasa harkar Cocoa ta hanyar sarrafa alawa dan yin kasuwancita a kasar Ghana.

Verarbeitung von Kakaobohnen in Ghana (dpa - Bildarchiv)

Su dai wannan matasa wadandan 'yan mata ne na zaune a kasar Switzerland kafin su yanke hukuncin komawa gida don kafa kamfanin wanda shi ne na farko a kasar ta Ghana. Guda daga cikin matan mai suna Kim Addison ta shaidawa DW cewa "mahaifinmu ya yi mana magana kan kasuwanci, wanda kuma hakan ya zaburar da mu har ya kai mu ga hana ido bacci. Mun yanke shawarar idan iyayenmu sun bar aiki a Switzerland sun komo Ghana muma za mu bi su. A don haka muka yi la'akari tasirin Alawa a Switziland duk da cewa ba su noman Cocoa, amma Ghana suna nomanshi amma ba su sarrafa alawa."

Matasan dai sun sawa masana'antar sarrafa alawar ta su sunan 57, sunan da ya samo tushe daga shekarun samun 'yancin kasar. To sai dai Priscilla mai shekaru 30 da ce matakan sarrafa alawar a cikin gidan mahaifin su na zama babbar kalubale da a yanzu ya musu tirniki inda ta ke cewar "babban kalubalen mu shi ne wutar lantarki a kasar Ghana da kuma sanin yanayin Ghana na zama abin mai wahala a garemu."

A yanzu dai ana sayar da alawar tsakanin euro daya zuwa euro biyar wato tsakanin Cedi 5 zuwa 25 kenan na kudin Ghana. Matasan dai na hamdala da tafiyar kasuwancin alawar sannu a hankali, to sai dai sun ce burinsu bai tsaya ga samun riba kadai ba amma sauya labarin da ke cewa kasar Ghana ba su iya sarrafa albarkatun da suke da shi a fadin kasar.