Salva Kiir ya amince da shirin zaman lafiya | Labarai | DW | 26.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Salva Kiir ya amince da shirin zaman lafiya

Shugaban ya rattaba hannu a lokacin ziyarar shugabanin kasashen na Afirka zuwa birnin Juba na Sudan ta Kudu, duk da yana da tacewa a batutuwa da suka shafi raba madafun iko.

Südsudan Präsident Salva Kiir

Salva Kiir shugaban Sudan ta Kudu

Wasu shugabannin Afirka, sun taru a babban birnin Sudan ta Kudu inda suka sheda ganin shugaba Salva Kiir ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar Laraban nan, abin da ake ganin zai kawo karshen watanni 20 da kasar ta dauka tana fama da tashe-tashen hankula. Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban ya bukaci a bashi lokaci yayi nazari kana ya tattauna da masu bashi shawara kan wannan yarjejeniya.

Tun dai a makon jiya ne bangaren adawa bisa jagorancin Reik Machar ya rattaba nasa hannun kan wannan yarjejeniya da Majalisar Dinkin Duniya da Amirka suka yi barazanar cewa zasu kakabawa kasar takunkumi idan shugaba Kiir ya gaza amincewa da ita.

Barnaba Marial Benjamin ministan harkokin wajen Sudan ta Kudu ya ce shugaban ya rattaba hannu a lokacin ziyarar shugabanin kasashen na Afrika zuwa birnin Juba, duk da cewa yana da ta cewa a wasu batutuwa da suka shafi raba madafun iko da tsohon mataimakinsa Reik Machar.