Sake sabunta kayayyaki | Himma dai Matasa | DW | 25.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Sake sabunta kayayyaki

Wani matashi a Jihar Bauchi da ke Najeriya ya kirkiro fasahar sake sabunta tsaffin kayyakin da ake amfani da su domin kare muhalli.

Wani matashi Injiniya Abubabakar Bello Buba, ya yunkuro wajen tsabtace muhalli ta hanyar sarrarfa tsaffin kayayyaki da ake zubarwa a bola wanda kuma ke kawo sanadiyyar ambaliyar ruwa da dumamar yanayi.

Injiniya Abubabakar Bello Buba ya fito fili ya bayyana dalilansa na sarrafa tsaffin kayayayyaki da ke sanadiyyar jawo ambaliyar ruwa da dumamar yanayi da ake fama da su ba a Najeriya kadai ba har ma da duniya baki daya. Akwai dai ma'aikata da ke taimakawa kusan goma, duk matasa wadanda shekarunsu sun kama daga sha bakwai zuwa ashirin, su ne suke tantance irin wadannan kayayyaki, suna kuma masu alfahari da wannan aiki kamar yadda suk ayi bayani suna cewa Abubakar ya ce zai so gwammnati ta lura da irin wannan kokari da suke yi saboda zai iya kawo aikin yi ga matasa da kuma kyautata muhalli.