1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Hada-hadar man fetur ta dawo

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
July 10, 2020

Libiya ta sake dawo da harkokin hakar man fetur dinta watanni shida bayan dakatar da aikin sakamakon tsanantar kai hare-hare da suka daidaita aikin.

https://p.dw.com/p/3f7dG
Libyen - Libyen - Öl Raffinerie in Cyrenaica
Hoto: picture alliance/AA/M. Elshaiky

Ma'aikatar man fetur din kasar ta Libiya ta sanar da cewa tuni wani jirgin ruwan dakon danyen man da ya kamata ya soma aikin jigilar man ya dire a gabar tekun al-Sedra mai albarkatun danyen mai a yankin gabashin kasar.

Sai dai rahotanni sun ce duk da sake dawowa da hada-hadar aikin danyen man, kasar ta Libiya za ta shafe tsawon lokaci kafin ta kai ga samar da ganga miliyan daya da digo biyu na danyen mai a kowace rana kamar yadda aka saba, duba da mummunar illa da ma koma bayan da kamfanin hakar man fetur din kasar ya fuskanta sakamakon tashe-tashen hankulan.