1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan jami'an Amirka da Koriya ta Arewa sun gana

Suleiman Babayo MNA
May 31, 2018

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya gana da Kim Yong Chol babban jami'in gwamnatin Koriya ta Arewa gabanin tattaunawar shugabannin kasashen.

https://p.dw.com/p/2ygpa
USA | US-Außenminister trifft nordkoreanischen Gesandten
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/Pool/File/M. Lee

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya gana tare da Kim Yong Chol tsohon babban jami'in leken asiri na Koriya ta Arewa kana na hannun daman Shugaba Kim Jong-Un inda mutanen biyu suka tattauna bisa shirin ganawa tsakanin shugaban biyu wadda za a yi a Singapore a watan Yuni. Babban jami'in na Koriya ta Arewa ya isa birnin New York na Amirka daga birnin Beijing na China inda ya fara ziyara.

Ana sa ran wannan tattaunawar za ta share hanyar ganawa tsakanin Shugaba Donald Trump na Amirka da takwaransa Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa a ranar 12 ga watan na Yuni. Babban bukatar Amirka ita ce kasar Koriya ta Arewa ta yi watsi da makaman nukiliya domin samun musanye da janye takunkumin karya tattalin arziki.

A wani labarin makamancin wannan ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya isa birnin Pyongyang na Koriya ta Arewa kamar yadda kafofin yada labarai suka bayyana gabanin ganawar da aka tsara tsakanin shugabannin Koriya ta Arewan da Amirka.

Ba a yi karin haske game da tattaunawar da ministan harkokin wajen na Rasha ya yi da jami'an kasar na Koriya ta Arewa ba. Shi dai Sergey Lavrov ya kai ziyarar farko a Koriya ta Arewa cikin shekara ta 2009.