1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres ya ji koken 'yan Rohingya

Abdul-raheem Hassan
July 2, 2018

'Yan gudun hijirar Rohingya da ke samun mafaka a Bangladesh, sun koka wa sakatare janar na MDD halin kunci da suka shiga sakamakon kisan gilla da cin zarafi da ya wuce kima da suka fuskanta daga sojojin Myanmar.

https://p.dw.com/p/30gGL
Antonio Guterres UNHCR
Sakatare Janar na MDD Antonio GuterresHoto: dapd

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ya ce a ganawar sa da wasu 'yan gudun hijira a sansanonin kasar Bangladesh, sun nuna bukatar samun adalci da kuma neman hukumomi maidasu gidajensu na asali. Sai dai kungiyar agaji ta Red Cross da ta ziyarci jihar Rakhine a baya-bayan nan, ta nuna shakku kan tanadin tsaro da walwalar jama'a da zai ba da damar dawo da 'yan gudun hijhirar a nan kusa.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta 'yan Rohingya 700,000 ne fargabar cin zarafi da tsinin bindiga tare da kisan gilla daga jami'an tsaron gwamnatin Myanmar, ya tilasta musu hijira zuwa kasar Bangladesh. A watan Nuwamban shekarar 2017 kasashen Bangladesh da Myanmar sun cimma yarjejeniyar fara maida 'yan gudun hijirar, amma rashin tsaro ya haddasa jan kafa a fara aiwatar da shirin.