Sakamakon zaben raba gardama a Girka | Siyasa | DW | 05.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon zaben raba gardama a Girka

Sakamakon kuri'ar raba gardama da aka kada a Girka na nuni da cewa masu goyon bayan muradin gwamnatin kasar na yin adawa da matakan tsuke bakin aljihu na dab da samun nasara.

Masu adawa da matakan tsuke bakin aljihu sun fara murna a Girka

Masu adawa da matakan tsuke bakin aljihu sun fara murna a Girka

Rahotanni sun tabbatar da cewa wadanda suka kada kuri'ar kin amincewa da matakan tsuke bakin aljihun sun lashe kaso 60 cikin 100 na kaso 20 daga kuri'un da aka rigaya aka kidaya yayin da kaso 40 suka kada kuri'ar amincewa. A wannan Lahadin ne dai al'ummar kasar Girkan suka kada kuri'a a zaben raba gardamar da gwamnatin kasar ta kira bayan da ta kasa biyan dinbin basussukan da masu bayar da bashi ke binta cikin wa'adin da aka dibar mata. Gwamnatin dai ta yanke shawarar kiran zaben raba gardamar nesakamakon wasu sababbin sharudda da masu bayar da bashin suka gindaya mata kan kara daukar matakan tsuke bakin aljihu kafin su kara bata wani bashin da take nema domin farfado da tatalin arzikin kasar, matakan da mahukuntan Girkan suka sanya kafa suka yi fatali da su. Ana sa ran a gobe Litinin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta tafi zuwa birnin Pari na kasar Faransa domin ganawa da Shugaba Francois Hollande kan sakamakon zaben Girkan.