1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben Bangaladash

December 31, 2018

Hukumar zaben kasar Bagaladash ta ce jam'iyyar Firaministar kasar ta Awami League, ta lashe zabe da gagarumin rinjaye.

https://p.dw.com/p/3AoJf
Premierministerin Bangladesch Scheich Hasina
Hoto: picture-alliance/Photoshot

A cewar hukumar a safiyar wannan Litinin, jami'yyar Awami League ta sami kujeru 288 daga cikin 300 da ake da su a majalisar kasar, abin da ya bada rinjayen mai karfi. 

Dama dai an yi hasashen samun galabar, duk da cewar an yi ta zargin magudi da kuma tashin rigingimu a wasu wuraren, inda rahotanni suka tabbatar da mutuwar akalla mutum 16.

An dai yaba kamun ludayin firaminista Sheikh Hasina, wacce ke shirin ci gaba da mulki a wa'adi na uku a Bangaladash ta fuskar kyautatuwar tattalin arziki.

Firaministar ta kuma sami yabo saboda karbar dubban musulmin da suka tsere wa rikicin kasar Bama, sai dai an zarge ta da matsa wa 'yan jarida.

Abokin adawarta Kamal Hossain dai, bai amince da sakamakon ba yana mai kiran a sake zaben.