Sakamakon zaɓe ya zo da gardama a Nigeria | Labarai | DW | 16.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaɓe ya zo da gardama a Nigeria

Tashe-tashen hankulla na ci gaba da ɓarkewa a sassa daban-daban na Nigeria,bayan bayyana sakamakon zaɓen yan majalisun jihohi da na gwamnoni.

A jihohi da dama, magoya jami´yun adawa, sun yi ta ƙone ƙonen tayoyi, gigaje,da motaci, domin bayyana fushin su, a kann abun da su ka ce maguɗi, da gwamnatin PDP ta shirya, don lashe zaɓen.

A halin yanzu, daga jihohi 14, da hukumar zaɓe ta riga ta bayyana sakamakon su, Jam´iyar PDP ta lashe zaɓen 11.

A kussan ko ina, jam´iyun adawa, sun yi watsi da sakamakon, sun kuma buƙaci shirya wani saban zaɓe.

A nata ɓangaren, humumar zaɓe mai zaman kanta INEC, ta bayyana gamsuwa da zaɓen.

Saidai ta soke na jihar Imo, wanda ta tabbatar da cewar ya na cike da magudi.

A wannan jiha za a shirya saban zaɓe ranar 28 ga watan da mu ke ciki.

A jihar Kano, inda magoya bayan jam´iyun adawa, su ka yi kwanan zamne, a harabar hukumar a zaɓe,a sahiyar yau ne, a ke kyauttata zaton bada sakamakon.