Sakamakon zaɓe ya tada hasumi a Zambia | Labarai | DW | 02.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaɓe ya tada hasumi a Zambia

A ƙasar zambia hukumar zaɓe mai zaman kanta, ta bayyana sakamakon wucin gadi, na zaɓen shugaban ƙasa.

Wannan sakamako,ya ce shugaba mai ci yanzu, Levy Mwanawasa, ya samu kashi 42 bisa 100, sannan abokin hamayar sa, Micheal Sata, ya tattara kashi 27 bisa 100.

Saidai sakamakon ya shafi mazaɓu 120, daga jimmilar mazaɓu 150 na faɗin ƙasar baki ɗaya.

Jim kaɗan bayan bayyana wannan sakamako, rikici ya ɓarke, tsakanin jami´an tsaro, da magoya bayan ɗan takara Micheal Sata, inda su ka ƙone motocin yan sanda a birnin Lusaka.

Su na zargin an tabka masu maguɗi, domin sakamakon farko da a ka bayyana, ya ba ɗan takara su rinjaye.

Shugaban ƙasa yayi kira ga al´umma ta kwantar da hankali.

A nata ɓangare, hukumar zaɓe mai zaman kanta,ta alƙawarta bada sakamakon ƙarshe na zaɓen a yau litinin, a game da haka, an tsaurara matakan tsaro a Lusaka, da sauran manyan birane na ƙasar.