Sakamakon wucin gadi na zaɓen Somalia | Labarai | DW | 15.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon wucin gadi na zaɓen Somalia

Jam´iyar APC mai adawa a ƙasar Saleo, ta yi iƙirarin lashe zaɓen yan majalisun dokoki, da ya wakana ranar asabar da ta wuce.

Shugabanin jam´iyar sun bayyana samun sakamakon dukan runfuna zaɓen ƙasar, wanda ya basu damar samun kujeru 61 daga jimmilar kujeru 112 da ka zaɓa.

Sannan ACP ta tabbatar da cewa, ɗan takara ta, a zaɓen shugaban ƙasa har yanzu na kann gaba.

Saidai ya zuwa yanzu hukumar zaɓe mai zaman kanta, ba ta bada sakamakon ba a hukunce.

Sakamakon wucin gadi da ta hiddo, tun daren jiya, ya shafi kashi 20 bisa 100 kawai na runfunan zaɓen ƙasar.

Shugabanin Jam´iyar ACP sun yi hannun ka mai sanda, ga hukumar zaɓen, tare da gitta barazanar gudanar da zanga-zanga, muddun ta bayyana sakamakon´da ya sha banban da wanda su ka tattara.