1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon bincike Amirka kan Siriya

August 30, 2013

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce Amirka na da tabbacin cewar Assad ne ya yi amfani da makamai masu guba bisa ga cikakken bincike da suka gudanar.

https://p.dw.com/p/19ZIi
US Secretary of State Kerry holds a press conference at Foreign Ministry concerning the intervention of Egyptian security forces in Cairo, Egypt. Bariskan Unal - Anadolu Agency
Kerry PressekonferenzHoto: picture alliance / AA

Amirka ta ce ta tabbatar gwamnatin Assad ce ke da hannu a wajen amfani da makamai masu guba a ƙasar wanda ya kashe sama da mutane dubu da ɗari hudu suka rasu, ciki har da kananan yara.Sakataren harkokin wajen Amirkan John Kerry ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi a wannan Jumma'ar inda ya ƙara da cewar Siriya ta fi kowacce ƙasa a yankin Gabas ta Tsakiya yawan makamai masu guba.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da Amirkan ke shirin afkawa Siriyan da yaƙi, inda Mr. Kerry ya ce matakin da za su ɗauka kan ƙasar zai zama tamkar aike wa da sako ga ƙasashe irin su Iran da kuma ƙungiyoyi irin su Hezbollah, sai dai ya ce ba za su bari abinda ya faru a Iraki ya maimaita kansa ba.

A daura da wannan, jami'an Majalsiar Ɗinkin Duniya da suka gudanar da bincike kan zargin amfani da makamai masu guba a yaƙin Siriya sun ce sun kammala bincikensu. Mai magana da yawun Majalisar Ɗinkin Duniya Martin Nesirky ne ya shaida hakan a wannan Jumma'ar, inda ya ƙara da cewar jami'an za su bar Siriya domin komawa bakin aikinsu don yin nazari kan shaidun da suka tattara kafin daga bisani su fidda sakamakonsu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane