Sakamakon ayyukan taimako a wata daya bayan tsautsayin Tsunami | Siyasa | DW | 26.01.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon ayyukan taimako a wata daya bayan tsautsayin Tsunami

Tuni mutane suka fara bayyana ra'ayinsu a game da ayyukan taimakon da ake gabatarwa yau wata daya bayan afkuwar tsautsayin nan na Tsunami

Wata daya bayan afkuwar girgizar kasar karkashin tekun da ta haddasa mahaukaciyar igiyar ruwan nan ta tsunami mutane da dama sun fara tofa albarkacin bakinsu a game da hada-hadar taimakon da aka gabatar. An saurara daga wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Indonesiya yana mai fadin cewar wannan bala’i ya taimaka aka samu kusantar juna tsakanin mutane daga sassa dabam-dabam na duniya. Ana kuwa bukatar irin wannan kusantar domin kare makomar wannan yanki na duniya daga bala’o’i da kuma wauta irin ta dan-Adam. Ba shakka kusan dukkan kasashe suka mayar da martani akan bala’in na tsunami, inda kasa kamar Australiya tayi alkawarin taimakon kudi na dala miliyan 800, ita kuma Jamus ta ce zata ba da taimakon dala miliyan 670 a yayinda China ke da niyyar ba da taimakon dala miliyan 85, a baya ga taimakon da daidaikun mutane suka bayar. Babu da wata matsala ta karancin kudin da ake fama da ita dangane da ayyukan taimakon da kuma ‚yan sa kai masu tarin yawa dake taimakawa bisa manufa. Har yau akwai kungiyoyin taimako na kasa da kasa dake ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankunan da bala’in ya rutsa dasu. Amma a inda take kasa tana dabo, kamar yadda kungiyoyin agajin ke korafi, shi ne yadda akan jibge kayan taimakon ba tare da an raba su tsakanin jama’a ba. Babban misali shi ne garin Banda Aceh dake kuryar arewacin lardin Sumatra, inda aka kafa tantuna da wuraren neman magani, amma ba majiyyatan da za a duba lafiyarsu. A yayinda a lokaci guda akwai dubbannin mutanen dake bukatar taimako ruwa a jallo a sauran sassa na gabar tekun lardin ba kuwa tare da taimakon ya kai garesu ba. Hakan dai na mai yin nuni ne da irin gibin dake akwai a matakan hada kan ayyukan taimakon. A baya ga haka ita kanta gwamnatin Indonesiya tana da dimbin sojojinta a yankin dake fafatawa da kungiyar tawaye ta Gam mai neman ballewa daga Indonesiya. Dukkan wadannan abubuwa na taimakawa wajen hana ruwa gudu ga ayyukan taimakon. Akwai dai masu tattare da kwarin guiwar cewa za a samu wani kyakkyawan ci gaba a kokarin shawo kan yakin basasar lardin Aceh nan da karshen watan fabarairu mai kamawa. Kasar Singapore ta janye sojojinta dake taimakawa tana mai dora alhakin ci gaba da wadannan ayyukan akan kungiyoyin taimakon jinkai. Hatta wasu daga cikin kungiyoyin taimakon masu zaman kansu sun janye daga yankin in-banda wasu kungiyoyin dake da nasaba da manufofin addini, wadanda a hakika ba a bayar da la’akari da su. Ci gaban da za a samu game da makomar ayyukan taimakon dai, kamar yadda manazarta suka nunar, ya danganta ne da take-taken mahukuntan Indonesiya, wadanda wajibi ne su dawo daga rakiyar manufofinsu na dogon Turanci. Wani ma’aikacin kungiyar taimakon jinkai ta CARE da ake kira Carsten Völz dai ya sikankance cewar matakan taimakon za a yi tsawon shekaru biyar masu zuwa ana gabatar da su.