1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka ta Kudu

Sakamako ya fara fitowa a zaben Afirka ta Kudu

May 30, 2024

Sakamako ya fara samuwa daga zaben kasar Afirka ta Kudu da aka kammala a ranar Laraba, zaben da jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ke fuskantar barazanar rasa rinjayenta tsawon shekaru.

https://p.dw.com/p/4gROE
Yadda ake tattara sakamakon zabe a Afirka ta Kudu
Yadda ake tattara sakamakon zabe a PretoriaHoto: Phill Magakoe/AFP/Getty Images

An soma samun sakamakon farko na zaben da aka yi a kasar Afirka ta Kudu, zaben da takara ta yi zafi a cikinsa a ranar Laraba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an makara wajen kada kuri'u a jiyan, inda wasu rumfunan zabe suka kasance a bude har cikin dare.

Kuri'un jin ra'ayin jama'a dai na ci gaba da nuna yiwuwar jam'iyyar ANC mai mulki na iya rasa rinjayen da take rike da shi a karo na farko cikin shekaru 30.

Hakan dai na nufin lallai ne jam'iyyar ta shiga hadaka da jam'iyya ko ma wasu kananan jam'iyyu kafin ta iya mulkar kasar.

Koda yake alamu dai na ci gaba da nuna damar jam'iyyar ta samu kuri'u mafi rinjaye, abin da zai bai wa shugaba mai ci Cyril Ramaphosa damar dorewa kan mulki.