Sabuwar dambarwar siyasa a Burkina Faso | Siyasa | DW | 02.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabuwar dambarwar siyasa a Burkina Faso

Takaddama ta sake kunno kai tsakanin Firaministan Burkina Faso da rundunar sojojin kasar da ke tsaron lafiyar shugaban kasa.

Wannan takaddama ce ta sake kunno kai ne sakamakon kiraye-kirayen da wasu kungiyoyin farar hula wadanda ake zargi da hadin baki da Firaministan kasar suka fara yi na ganin an rusa wannan rundunar da ke gadin shugaban kasa, da 'yan kasar Burkina da dama ke kallo a matsayin wata barazana ga makomar demokradiyyar kasar.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai wasu sojoji membobin runduna ta musamman da ake kira RSP da ke tsaron lafiyar tsohon shugaban kasa Burkina Faso Blaise Compaore wacce kuma ke ci gaba da aiki duk da korar tsohon shugaban kasar, suka yi ta harba bindigogi a sama daga cikin barikinsu. A cewarsu sun yi haka ne domin nuna bacin ransu dangane da gaiyatar wasu daga cikin jagororinsu da hukumomi suka yi zuwa ofishin jami'an jendarma da zummar sauraransu a bisa zarginsu da neman shirya wata makarkashiya ga Firaministan kasar Isaac Zida wanda shi da kansa ya fito ne daga cikin wannan runduna ta RSP.

Cece kuce tsakanin sojoji da fadar mulki

Burkina Faso Premierminister Isaac Zida 21.11.2014 Ouagadougou

Firaministan Burkina Faso Isaac Zida

Wasu masu lura da harkokin siyasar kasar na cewa rundunar ta yi amfani da karfin da ta ke da wajen tilasta zaben Isaac Zida a matsayin Firaministan riko na kasar. Rundunar sojojin ta RSP dai na mai zargin Firaministan da cin amanarta ta hanyar fakewa da wasu kungiyoyin farar hula na kasar wadanda a 'yan kwanakin nan suka soma yin kiraye-kirayen ganin an rusa wannan runduna domin cimma burinsa na rusa rundunar, abunda Isaka Lingani daraktan jaridar L'opinion mai zaman kanta da ke a kasar ya ce biri kam ya yi kama da mutun.

"Mutane da dama ne ke tambayar kansu in har ba wata makarkashiya ba ce aka shirya domin shafa wa wannan runduna kashin kaji musamman ta hanyar yin amfani da wasu kungiyoyin farar hula da kowa ya sani na rawa da bazar wasu sanannuin 'yan siyasa domin neman ganin an rosa wannan runduna."

To ayar tambaya dai ita ce wadanne dalillai ne ke sawa Firaministan ya nemi ya rusa rundunar da ita ce ta kai shi a matsayin da ya ke a yau. A kan wannan batu Isaka Lingani ya bada amsa yana mai cewa.

"Kwadayinsa a bayyane yake cewa na farko yana son a tsawaita wa'adin mulkin rikon kwarya wanda a ko ina a yau zancan ake. Sannan akwai maganar tsaron lafiyarsa domin matsawar wannan runduna na raye kuma shi yana tunanin cewa ya ci amanarta to kuwa ba ya fatan ganin wannan runduna ta rayu bayan mulkinsa."

Matasa ka iya sake bazuwa kan titi

Burkina Faso Bürgerbewegung Le Balai citoyen

Kungiyar jama'a ta Le Balai Citoyen. A hagu mawaki Rap Smockey

Shahararren mawakin nan na kasar Burkina Faso Smockey daya daga cikin jagororin kungiyoyin farar hula masu da'awar tsabtace kasar da kuma suka jagoranci zanga-zangar da ta kai ga korar shugaba Blaise Compaore na ganin ko a yanzu dole matasa da sauran 'yan kasar su sake zare damtse.

"Ba mu zo da gugar takalmin wani ba dan haka ina ganin matasa da sauran masu mulki da duk masu karfin iya kawo canji su dauki mataki a kan al'amuran na yau."

Yanzu dai 'yan kasar ta Burkina Faso da ma sauran kasashen duniya sun zura ido su ga yadda wannan sabuwar takaddama da ta taso a fagen siyasar kasar za ta kaya.

Sauti da bidiyo akan labarin