Sabon yunkurin warware rikicin Siriya
January 31, 2013Wata sanarwar da fadar shugaban Amirka ta White House ta fitar a wannan Alhamis (31.01.13), ta nunar da cewar mataimakin shugaban na Amirka Joe Biden zai tattauna hanyar kawo karshen rikicin Siriya tare da ministan kula da harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da kuma jagorar 'yan adawar kasar ta Siriya Moaz al-Khatib a wannan Asabar. Biden, zai yi wannan ganawar ce a gefen babban taron da zai mayar da hankali akan lamuran tsaro a birnin Munich na nan Jamus, wanda kuma zai bashi damar tattaunawa tare da shugabannin Jamus da Faransa da kuma Birtaniya.
Taron dai na zuwa ne bayan da wasu rahotannin da ba'a tabbatar da su ba na nuna cewar Isra'ila ta kaddamar da hari akan wata cibiyar biciken makamai ta soji da kuma wani jerin gwanon motocin da ke dauke da makamai akan iyakar Siriya da Lebanon.
A dai wannan alhamis ne gwamnatin kasar ta Amirka ta yi gargadi game da yiwuwar gwamnatin Siriya ta mikawa mayakan kungiyar Hizbullahi da ke kasar Lebanon, wasu daga cikin makaman da ta mallaka.
A can baya dai Amirka ta yi Allah wadai da rasha game da hawan kujerar na ki ga wasu kudurorin Majalisar Dinkin Duniya akan Siriya.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou