Sabon yunkurin warware rikicin Afirka ta Tsakiya
January 23, 2014Talla
Masu ruwa da tsaki a sha'anin tafiyar da harkokin mulki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun zabi Catherine Samba-Panza a matsayin shugabar rikon kwarya, inda ta bukaci samun goyon bayan 'yan kasar da kuma al'ummomin kasa da kasa wajen shawo kan rigingimun dake addabar kasar, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu kuma suka tsere daga matsugunansu.
Ko da shike mutane da dama sun yi fatan murabus din da tsohon shugaban wucin gadin kasar Michel Djotodia zai taimaka wajen kwantar da wutar rikicin, amma kuma har yanzu Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyan na fama da rgngimun dake da nasaba da addini da kuma kabilanci.