1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunkurin kawo karshen yakin basasar Siriya

October 6, 2013

Manzon Majalisar Dinkin Duniya a rikicin Siriya ya ce babu alamar kawo karshen rikicin kasar a nan kusa.

https://p.dw.com/p/19uRb
U.N. Special Representative Lakhdar Brahimi makes a statement to the media after hosting a meeting between U.S. Secretary of State John Kerry and Russian Foreign Minister Sergei Lavrov discussing the ongoing crisis in Syria at the United Nations offices in Geneva, September 13, 2013. REUTERS/Larry Downing (SWITZERLAND - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Babban mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen Larabawa a rikicin Siriya, Lakhdar Brahimi, ya jaddada cewar, ba shi da tabbas game da yiwuwar gudanar da taron neman sulhu ga rikicin, kamar yadda kasashen duniya suka tsara yi a birnin Geneva a tsakiyar watan Nuwamban da ke tafe. A lokacin da yake amsa tambayar da tashar telebijin ta TV5 da kuma gidan Rediyon RFI na Faransa suka yi masa, Brahimi ya ce babu tabbas, sai dai kawai yana mika goron gayyata ne kawai ga masu ruwa da tsaki cikin lamarin, kuma yana karfafa musu gwiwar su halarci taron. Dama tun a ranar Talatar (01. 10. 13) da ta gabata ce, Brahimi ya ce ba shi da yakini 100 bisa 100 dangane da yiwuwar taron.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman